Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - nakalto lauya mai kare wadanda ake tuhuma Tresor Kabangu, yana cewa mafi yawan wadanda aka yankewa hukuncin basa hannu.
Labarin ya kara da cewa, Zaida Catalan ‘yar kasar Sweden da kuma Michael Sharp dan kasar Amurka sun hadu da ajalinsu ne a lokacinda ‘yan bindiga suka taresu a kan hanya sannan suka shiga da su daji suka kashesu.
Jami’an MDD biyu suna bincike ne kan rikicn da ya faru tsakanin sojojin kasar Congo da yan bindiga a yankin Kasai na kasar ta Congo wanda ya kai ga mutuwar mutane da dama.
Amma dangin mutanen biyu sun ce har yanzun suna ganin ba’a hukunta wadanda suke da hannu a kisan daga cikin manya-manyan mutane a kasar ba.
342/